Kungiyar 'Yan Jaridu Ta Jihar Yobe Ta Samarda Yanayin Zaman Lafìy Tsakanin Manoma
Daga Sani Gazas Chinade Damaturu
Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya reshen jihar Yobe (NUJ) ta kaddamar da wani gagarumin shirin samar da zaman lafiya ta hanyar wayar da kan jama’a musamman cibiyoyin gargajiya na jihar domin magance rikice-rikicen manoma da makiyaya.
Da yake jagorantar wannan yunkurin, Shugaban kungiyar 'yan jaridu (NUJ) na Jiha Kwamared Rajab Mohammad Ismael ya jagoranci tawagar ‘yan jarida zuwa wasu manyan sarakunan gargajiya, inda tawagar ta gana da sarakunan Fika, Alhaji Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idrissa, Bade, Alhaji Abubakar Umar Sulaiman da na Masarautar Jajere, Alhaji Mai Hamza Buba Ibn Isa Mashio a fadarsu.
Tawagar ta NUJ ta gana kai tsaye da wadannan Sarakunan iyayen qasa waxanda aka san su a matsayin masu kula da al’adu da zaman lafiya tare da shiga tsakanin masu rikici da juna a masarautunsu.
Tattaunawar tasu ta ta’allaka ne kan samar da ingantattun dabaru don dakile tashe-tashen hankula tsakanin manoma da makiyaya da ake yawaita samu lokaci zuwa lokaci.
Da yake jawabi a fadar Mai Martaba Sarkin Fika, Alhaji Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idrissa, shugaban na NUJ komred Rajab Ismael ya jaddada muhimmiyar rawar da kafafen yada labarai ke takawa.
Ya ce dole ne kafafen yada labarai su wuce bayar da rahoton abubuwan da suka faru kawai don samar da fahimta da gina zaman lafiya mai dorewa a tsskankanin al'umma.
“Manufarmu ta ziyartar fadar ma su Martaba sarakunan Fika, Bade, da Jajere ita ce wayar da kan al’ummar kan illolin da ke tattare da wannan rikici da kuma lalubo hanyoyin hadin gwiwa don samun zaman lafiya,” in ji Shugaban NUJ.
Ya jaddada tasiri na musamman na Masarautar wajen kaiwa ga al'ummomin kasa da inganta tattaunawa mai mahimmanci.
Rajab Isma'el ya yi qarin haske da cewa gangamin na da nufin wayar da kan jama'a game da munanan illolin da yawaitar faxace-faxacen ke haifarwa.
Yin hakan na matuqar yin tasiri ta hanyar kwantar da hankali na al'umma, tattalin arzikin jihar mai rauni kan iya farfaxowa da hadin kan al'umma gaba daya.
Ya bayyana irin rawar da shugabannin al’umma da sarakunan gargajiya ke takawa wajen sasanta rigingimu da wuri, kafin su rikide zuwa mummunan tashin hankali.
Da yake mayar da martani, Mai Martaba Sarkin Fika, Mohammed Abali Ibn Muhammadu Idrissa, ya yi maraba da wannan shirin wannan kungiya ta NUJ, ya kuma yaba wa ‘yan jarida bisa jajircewar da suke yi da kuma yin fito-na-fito da mummunan tasirin rikicin manoma da makiyaya a yankunansu ta wajen wayar da kan al'ummomi don a kaucewa hakan.
"Na ji daɗin jin labarin nasarorin da kuka samu da kuma nuna godiya ga kyakkyawan aikinku, musamman a cikin rahotanni ku game da abubuwan da suka faru ko suke faruwa da rubuce-rubucen ku.
"Muna taya ku murna kan nasarar da kuka samu na bayar da rahoto dai-dai kuma ba tare da sava ka'ida ba.
Muna sane da matsalolin da kuke fuskanta a wasu lokuta a cikin rahoton ku yadda wasu mutane, ciki har da gwamnatoci a wasu lokuta, ba sa farin ciki a ko da yaushe da yadda kuke gudanar da ayyukan ku wajen bin gaskiya ba tare da voye labari ba.
"Duk da haka, kun tsaya kan gaskiya kuma kun yi rahoton karara, muna jin dadin aikinku," in ji Sarkin Fika.
Shi ma da yake jawabi a fadarsa, Sarkin Bade, Alhaji Abubakar Umar Sulaiman ya ce, “Daga cikin matakan da Masarautar take dauka na dakile rikicin manoma da makiyaya sun hada da hana makiyaya kiwo bayan karfe 6 na yamma, da hana su tura kananan yara kiwon dabbobi, da hana manoma yin noma a hanyoyin hijirar dabbobi, da dai sauransu a fadin masarautar ta Bade.
“Mun kuma kafa tawagogin sintiri na musamman da za su rika lura da gonaki da kuma tantance halin da ake ciki a idon duniya, gwamnati ta samar da wuraren kiwo a Masarautar mu da suka kunshi asibiti, makaranta, da rijiyar burtsatse, mun yaba da hakan, amma muna rokon a gina karin wuraren mashayar ruwa da kuma dajin kiwo son ciyar da dabbobin,” in ji Basaraken na Bade.
Dukkanin sarakunan da suka ziyarce su sun yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya ga Majalisun Masarautar su wajen tabbatar da zaman lafiya da himma wajen wayar da kan manoma da makiyaya da ke karkashinsu kan bukatar tattaunawa da mutunta juna cikin gaggawa.

Comments
Post a Comment