Matashi Ya Kashe Maƙwabcinsa Saboda Rigimar Igiyar shanyar Katsina
Wani matashi mai shekaru 35 da haihuwa, mai suna Aminu daga karamar hukumar Ingawa ta jihar Katsina, ya kashe maƙwabcinsa Malam Masa’udu mai shekaru 45 da wuƙa, bayan wata sa’insa da ta barke tsakaninsu da yammacin Alhamis, ranar 3 ga watan Yuni, 2025.
Lamarin ya faru ne a unguwar Ministerial Quarters kusa da Fatima Shema Estate da ke cikin birnin Katsina, inda duka biyun ke zama kuma ke gudanar da sana’ar wanki da guga.
Ganau sun bayyana cewa rigimar ta samo asali ne daga igiyar da ake amfani da ita wajen shanya kaya a bakin shagunan da suke haya, wadda Malam Hassan ya daura don amfanin kowa. Malam Masa’udu dai ya nemi yin amfani da igiyar, sai dai Aminu ya hana shi, yana mai cewa ba shi da ikon shanya kayan a wurin.
“Masa'udu yace kayi hakuri in shanya kayan tunda dai ba kai ka ɗaura igiyar ba, kuma dai ba wani dadewa za su yi ba." Amma Aminu ya ce ko ni da na sa igiyar ban isa na bari a shanya kayan ba, sai ya jefar da kayan ƙasa, ya tattaka su da ƙafa,” in ji Malam Hassan mamallakin igiyar, wanda ya shaida faruwar lamarin.
Bayan haka, Malam Masa’udu ya shiga wani shago yana faɗa wa mutane abin da ya faru. Amma cikin zafin rai, Aminu ya biyo shi da wuƙa. Duk da cewa Malam Masa’udu ya yi ƙoƙarin tserewa, Aminu ya bi shi har ya cimma shi, inda ya daba masa wuƙa sau da dama – wasu ganau sun ce sau bakwai.
An garzaya da shi zuwa Asibitin K-Dara da taimakon jami’an hukumar NSCDC, amma ya rasu kafin a kai shi asibiti. Daga bisani aka mayar da gawarsa zuwa babban Asibitin Katsina tare da taimakon DPO na 'yan sanda na Charanci, wanda ya tuntubi jami’an tsaro na Batagarawa da suka cafke wanda ake zargi.
A ranar Juma’a, 4 ga Yuni 2025, aka yi jana’izarsa a gidansa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Binciken ya gano cewa ba wannan ne karo na farko da aka samu sa’insa tsakanin Aminu da Marigayin ba. A bara, kafin azumin Ramadan, Aminu ya zargi Masa’udu da yi masa sharri kan zargin Luwadi, wanda ya kai kara kotu. Sai dai kotun ta yi watsi da karar saboda rashin hujja mai karfi.
Marigayin wanda asalin dan karamar hukumar Kaita ne, ya shafe shekaru a unguwar Ministerial Quarters, kuma ya kasance mutum mai mutunci da amana, inda har ya ke kula da shagunan haya da lissafin kudin wuta da sauran lamurra a wajen. Shi ne ma ya ba Aminu shagon da yake haya kafin kisan ya faru.
Marigayi Malam Masa’udu ya bar mata daya da ‘ya’ya shida, yayin da Aminu wanda ba shi da aure ke tsare a hannun rundunar ‘yan sanda ta Katsina, a inda bincike ke ci gaba.

Comments
Post a Comment