Gwamnatin Jihar Katsina Ta Amince Da Kafa Sabuwar Tashar Zangon FM A Jihar

 

Daga Fatima Mukhtar 

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Katsina, Dakta Salisu Bala Zango, ya bayyana cewa gwamnati ta amince da kafa sabuwar tashar rediyo mai gajeren zangon FM a wannan shekarar.

Dakta Salisu Ya bayyana hakan ne yayin kare kasafin kuɗin ma’aikatarsa a matakin Maaikatar kula da kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki dake gudana a tsohuwar Fadar Gwamnati.

A cewar sa, aikin kafa tashar FM ɗin zai ci wa gwamnati kimanin naira miliyan 366, kuma ana sa ran hakan zai ƙara haɓaka inganci, yawan masu sauraro, da faɗaɗa isar da shirye-shirye da manufofin gwamnati.

“Mun samu amincewar kafa sabuwar tashar FM jiya, kuma muna cikin shirye-shiryen tabbatar da cewa ta fara aiki cikin wannan shekara,” in ji shi.


Kwamishinan ya bayyana cewa, da zarar an kaddamar da tashar FM ɗin, za a samu damar cika burin samun kudin shiga har naira miliyan 300 daga tashar AM mallakar jihar.


Haka kuma, kwamishinan ya bayyana shirin gwamnati na sanya samarwa gidan Radion jihar makamashi mai aiki da  hasken rana (solar power) domin inganta aiki.


“Muna cikin aiwatar da shirin sanya solar panels a babban ofishin tashar rediyo da reshe na Dutsinma domin rage kashe kuɗin dizal da kuma magance matsalar katsewar wutar lantarki daga  kamfanin KEDCO,” in ji shi.


Dakta Zango ya ƙara jaddada kokarin Gwamna Dikko Umar Radda wajen sauya fasalin tashoshin rediyo da talabijin na jihar zuwa tsarin zamani (digitalization).


Ya yaba wa gwamnatin jihar bisa umartar ma’aikatu da hukumomin gwamnati da su riƙa tallata ayyukansu ta hanyar talla da sanarwa a tashoshin jihar, tare da tabbatar da cewa duk wani kudin shiga da aka samu za a tafiyar da shi cikin gaskiya da adalci.

Comments

Popular posts from this blog

Matashi Ya Kashe Maƙwabcinsa Saboda Rigimar Igiyar shanyar Katsina

ADC Coalition Stuns Kaduna: Secures 2 of 3 Constituencies in Landmark Victory

A Champion for Change: Commendation to Alhaji Hamisu Ado, Education Secretary, Nguru