Hadarin Mota Ya Lakume Rayukan Mutum 7 A Hanyar Damaturu-Maiduguri


Daga Sani Gazas Chinade  Damaturu

Wani haɗarin mota da aka yi a ranar talata kan hanyar Damaturu- Maiduguri ya lakume rayukan akalla Mutane 7 yayin da wasu kuma suka Jikkata.


Kamar yadda bangaren motocin kai daukin  gaggawa ga majinyata da hadurra a Jihar ta Yobe ke cewa wannan hadarin ya faru ne tsakanin wata mota da ke dauke da fasinjoji kirar Toyota Sienna  da kuma karamar mota kirar Toyota Corolla akan hanyar ta Damaturu zuwa Maiduguri.


Kamar yadda wani shaidun gani da ido ke bayyanawa wakilinmu cewar wannan hadari ya afku ne sanadiyyar gudun wuce kima da direbobin ke yi wadda shi ya haifar da hakan.


Wannan hadari dai ya yi sanadiyyar salwantar rayukan Mutane kimanin 7 nan take yayin da wasu suka ji raunuka kamar yadda aka ambata a baya.


Haka nan kamar yadda rahoton ke nunawa wannan hadari ya faru ne a kusa da kauyen warsala da ke kan hanyar ta Damaturu zuwa Maiduguri.


Samun labarin afkuwar wannan mummunan hasari ke da wuya nan da nan jami'an motocin da gwamnatin Jihar Yobe ta ware don kai daukin gaggawa YEMABUS suka garzaya zuwa wurin tare da dauko gawawwaki da mutanen da suka Jikkata ya zuwa babban asibitin koyarwa na jami'ar Jihar Yobe (YSUTH) da ke Damaturu don kula da su cikin gaggawa.


Da ya ke tabbatar da hakan jam'in yada labarai na vangaren motocin dauko.marasa lafiyar cikin gaggawa (YEMSBUS) Ibrahim Waziri ya ce lalle wannan hadari ya faru ne sakamakon gudun wuce kima da direbobin ne ke yi.


A cewar sa ya zuwa yanzu dai wannan hadari ya yi sanadiyyar Mutuwar Mutane 7 ne hudu manya 3 kuma kananan yara yayin da wasu kuma suka jikkata.

Comments

Popular posts from this blog

Matashi Ya Kashe Maƙwabcinsa Saboda Rigimar Igiyar shanyar Katsina

ADC Coalition Stuns Kaduna: Secures 2 of 3 Constituencies in Landmark Victory

A Champion for Change: Commendation to Alhaji Hamisu Ado, Education Secretary, Nguru