Gwamnatin Yobe Zata Karrama Wadanda Suka Lashe Gasar Harshen Turanci, Muhawara Ta Duniya
Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnan jihar Yobe (Dr) Mai Mala Buni, ya amince da wani gagarumin biki na karrama Nafisa Abdullah ‘yar shekara 17 da Rukayya Muhammad Fema ‘yar shekara 15 a matsayin waxanda suka yi fice a duniya a fannin fasahar harshen Ingilishi da muhawara baki xaya a gasar cin kofin duniya na TeenEagle na shekarar 2025 a birnin Landan na qasar Birtaniya.
A wata sanarwa da Mamman Muhammad daraktan 'yan jaridu da harkokin yaxa labarai na gwamna ya sanar ya ce, Nafisa da Ruqayya dukkansu daga jihar Yobe xalibai ne na kwalejin qasa da qasa ta Tulip (Nigerian Tulip International College,) waxanda suka wakilci Najeriya a gasar cin kofin duniya inda suka doke sauran mahalarta 20,000 daga qasashe 69 na duniya.
Nafisa da Rukayya dukkansu sun ci gajiyar shirin tallafin karatu na Gwamna Mai Mala Buni wanda ya qunshi cikakken karatun dalibai 890 a Kwalejin qasa da qasa ta Najeriya Tulip.
Gwamna Buni ya bayyana wannan nasara da matasan suka samu a matsayin babban abin alfahari ga jiha da qasa baki xaya.
"Wadannan manyan ayyuka ne da ke sa mu yi alfahari da kuma tabbatar da saka hannun jarin gwamnati a fannin ilimi," in ji Gwamna Buni.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da bayar da tallafin karatu ga kowane yaro a jihar domin samun damar zuwa makaranta, ya kuma yi qira ga iyaye da su ba su haxin kai.
“Gwamnati ta sake gina makarantun da rikicin ya rusa, ta samar da kayayyakin karatu, litattafai, kayan aikin gwaje-gwaje da kuma xaukar qwararru malamai aikin yi domin inganta ingantaccen ilimi a jihar, kuma har yanzu aiki ne a kan ci gaban lamarin.” Inji shi.
A halin yanzu, akwai kimanin xaliban jihar Yobe 40,000 da ke samun tallafin karatu na gwamnati da ke karatun kwasa-kwasai daban-daban a Jami’o’i da sauran manyan makarantu a Najeriya da qasashen ketare.
Idan dai ba a manta ba a ‘yan watannin da suka gabata jihar ta yi bikin yaye xalibai 167 da suka ci gajiyar shirin tallafin karatu da jihar ta samu wadanda suka kammala karatunsu a fannin kimiyyar likitanci da na’ura mai qwaqwalwa da injiniyanci daga jami’o’in qasar Indiya

Comments
Post a Comment