Gwamna Buni Ya Jagoranci Tawagar Jiha Zuwa Jana'izar Sarkin Gudi
Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnan jihar Yobe (Dr) Mai Mala Buni a ranar Juma’a ya jagoranci tawagar gwamnati wajen jana’izar marigayi Sarkin Gudi, Alh. Isa Bunuwa Madugu Ibn Khaji, wanda ya rasu a wani asibiti da ke Abuja bayan ya sha fama da jinya.
A cewar Mamman Mohammad daraktan 'yan jaridu da harkokin yada labarai na gwamna Buni cikin takardar da ya sanyawa hannu kuma ya raba wa manema labarai ya ce gwamnan da ke halartar wani taro a Abuja ya yanke wannan ziyara ta sa domin halartar jana’izar marigayi Sarkin da kansa.
Gwamna Buni ya samu rakiyar kakakin majalisar dokokin jihar Yobe Alhaji Chiroma Buba Mashio, Sanata Ibrahim Mohammed Bomoi, Sanata Musa Mustapha, da 'yan majalisar wakilai.
Sauran sun hada da sakataren gwamnatin jihar Baba Malam Wali, ‘yan majalisar dokokin jihar, da kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman, shugabannin kananan hukumomi, Sarakuna, Malamai, jiga-jigan jam’iyya da dubban magoya bayansa.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa kurakuran sa, ya kuma yi kira ga al’umma da su tsaya tsayin daka, kuma su yafe wa juna, domin “kowa zai mutu, a yaushe ne, a ina da kuma wadda Allah Ta’ala ne kaxai ya sani.
Gwamna Buni ya bayyana rasuwar sarkin a matsayin babban rashi ga dangi, masarautar Gudi, jihar Yobe da kuma Najeriya baki daya.

Comments
Post a Comment