Dalibai 62 Ne Sukai Saukar Alqur'ani A Makarantar Shaharab



 

SHAHRAB International School, dake kusa da Rawul ɗin Barhim, a sashen Islamiyya, ta yaye Ɗalibai 64 da suka sauke Al-Qur'ani Maigirma, Mata 43, da kuma Maza 19.

Taron wanda ya kasance karo na 5, ya gudana a ɗakin taro na Mamman Sarkin Tanshi dake cikin makarantar.

Katsina Post ta samu cewa, shugabar makarantar a sashen Islamiyya, Dr. Nana Bature, ita ce ta jagoranci walimar domin ƙara ƙarfafa guiwa ga Ɗaliban a harakokin karatun su.

Lokacin gudanar da walimar, an ja kunnen Ɗaliban da su kasance ma su kula da karatun Alqur'ani Maigirma don kar su nemi shi su rasa, haka kuma, iyayen Yara sun gode ma makarantar da duk Malaman da suka ba Yaran su gudunmawa ta ilimi har suka sauke.

Comments

Popular posts from this blog

Matashi Ya Kashe Maƙwabcinsa Saboda Rigimar Igiyar shanyar Katsina

ADC Coalition Stuns Kaduna: Secures 2 of 3 Constituencies in Landmark Victory

A Champion for Change: Commendation to Alhaji Hamisu Ado, Education Secretary, Nguru