Shugaban Qasa Tinubu Ya Yabawa Buni Kan Bada Gagarumar Gudummawa Akan Harkar Noma
Daga, Sani Gazas Chinade Damaturu
Shugaban qasa Bola Ahmed Tinubu ya yabawa gwamnatin jihar Yobe bisa yadda ta zuba jari mai yawa a harkar noma domin tabbatar da wadatar abinci da tsaro a jihar.
Shugaban qasar ya bayyana haka ne a ranar a wajen qaddamar da shirin qarfafa aikin gona na jihar a filin wasa na 27 Agusta Damaturu babban birnin jihar.
Tinubu wanda babban mataimaki na musamman ga shugaban qasa kan harkokin siyasa da sauran su, Alhaji Ibrahim Kabiru Masari ya wakilta, ya ce shirin qarfafa ayyukan noma na jihar Yobe ya yi daidai da sabunta tsarin fatan gwamnatin tarayya kan havaka harkokin noma a qasar nan.
Ya kuma ba da tabbacin hadin gwiwar gwamnatin tarayya domin inganta ayyukan noma a jihar.
A jawabin sa yayin qaddamar da kayayyakin noman, Gwamnan Mai Mala Buni, ya ce gwamnatin jihar ta sayo taraktocin noma samfurin Massey Ferguson guda 40, kananan injunan bada hasken wutar lantarki 1,961, qananan garmunan noma na turawa da hannu guda 1,250, qananan injunan bayi guda 553 sai injunan bayi masu amfani da hasken rana 3,410, na'urorin feshin taki 830, buhunan takin zamani nau'in NPK 20-10-10 buhuna 4,500 da makamantan haka.
Hakazalika akwai ingantattun iri nau'i daban-dabam da irin doya rogo da kuma baburan Keke Napep guda 50 da babura 30 don shirin.
"A bisa tsarinmu na inganta ayyukan noma a jihar nan, ina ba da umarnin cewa, a raba injuna, kayan aiki da sauran kayan aikin gona kyauta ga manoman da suka cancanta.
Bugu da qari kuma, ina bayar da umarnin ba da tallafin kashi 50% kan siyar da takin zamani ga manoma," in ji Gwamna Buni.
Idan dai ba a manta ba a shekarar da ta gabata ne gwamnatin jihar Yobe ta sayo tare da raba taraktoci 100, injinan noman hannu, injinan ban ruwa masu amfani da hasken rana, injunan sissika iri-iri, ingantattun injunan shuke-shuke da taki da dai sauransu

Comments
Post a Comment