Kungiyar MEDCI Ta Jinjinawa Gwamnatin Yobe Kan Samar Da Hanyoyin Mota A Karkara

 


Daga Sani Gazas Chinade Damaturu 

Babban Daraktan kungiyar Media and Disability Care Initiative (MEDCI), wata kungiya mai zaman kanta, Malam Rajab Mohammed Isma’il, ya yabawa gwamnatin Yobe kan ayyukan gina tituna da take gudanarwa, musamman a yankunan karkarar jihar.

Daraktan kungiyar ya yi wannan yabon ne a ranar Asabar a Potiskum a lokacin da ya jagoranci tawagar ‘yan jarida a rangadin da ya kai wasu ayyukan gina tituna da gwamnatin jihar ke gudanarwa.

Daga cikin ayyukan da suka kai ziyara har da hanyar Potiskum zuwa Ngojin mai tsawon kilomita 2.5 da hanyar Fadawa zuwa Daya mai tsawon kilomita 5, dukkansu ma'aikatar ayyuka ta jihar ne ta aiwatar ta hanyar aiki kai tsaye.

Shugaban na MEDCI ya lura cewa hanyoyin suna da matukar muhimmanci ga ci gaban karkara kuma za su inganta hanyoyin kiwon lafiya, ilimi, da kasuwanni ga al’ummomin yankunan da akasarin su manoma ne.

Da yake jawabi a yayin ziyarar, shugaban al’ummar Ngojin B, Malam Bulama Haruna, ya nuna jin dadinsa ga gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni kan wannan matakin na gudanar da wadannan muhimman ayyuka na Gina hanyar mota a yankunan su.

Ya ce aikin gina titin ya kawo sauki ga mazauna yankin da a baya suka fuskanci matsalar shiga wasu yankunan musamman a lokacin damina.

“A baya min fuskanci matsaloli wajen sufuri musamman a lokacin damina, kusan ba zai yiwu a shiga ko fita daga Ngojin ba, amma sakamakon wannan cigaba da muka samu a yanzu komai namu zai gudana kamar yadda muke nema.” inji shi.

Wani mazaunin Ngojin, Abdullahi Mohammed, ya bayyana aikin hanyar a matsayin daya daga cikin abubuwan da suka fi tasiri a yankin cikin kusan karni.

Ya lura cewa hanyar mai tsawon kilomita 2.5 ta inganta jigilar kayan amfanin gona da kuma kai marasa lafiya zuwa ga asibitocin cikin sauki, ya kara da cewa noma ya kasance babban aikin al'ummomin wannan yanki namu.

Hakazalika, Malam Idi Muhammed Madaki, mazaunin unguwar Daya, ya yabawa gwamnatin Buni bisa aikin gina hanyar Fadawa zuwa Daya mai tsawon kilomita 5.

Ya ce al’umma sun dade suna jiran irin wannan ci gaban tun lokacin da aka kirkiro jihar Yobe, kuma tabbatar da aikin a lokacin gwamnati mai ci abu ne mai matukar muhimmanci.

“Mun gode wa Gwamna Buni da duk wadanda suka yi hakan, musamman kwamishinan ayyuka,” inji shi.

Shima da yake jawabi Injiniya Saleh Mustapha, Wanda shine  Injiniya Mai kula da  aikin hanyar Fadawa zuwa Daya mai tsawon kilomita 5, yace aikin yana tafiya kamar yadda aka tsara kuma za'a kammala shi cikin ka'idar da aka sa na kammaluwar aikin. 

Comments

Popular posts from this blog

Matashi Ya Kashe Maƙwabcinsa Saboda Rigimar Igiyar shanyar Katsina

ADC Coalition Stuns Kaduna: Secures 2 of 3 Constituencies in Landmark Victory

A Champion for Change: Commendation to Alhaji Hamisu Ado, Education Secretary, Nguru