Ibrahim Dan Alkalee Masari ya raba wa yan gudun hijirar kayan abinci na miliyoyin nairori a matsayin tallafi



Daga Sa'idu Dahiru (Commitment) 

Matashi dan kishin kasa da ci gaban ƙaramar hukumar Bakori, kuma dan kasuwa mai zaman kansa Alh Ibrahim Dan Alkali, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar One Good Turn Deserve Another Dikko/Tinubu 2027, a yau Alhamis ya ƙaddamar da rabon kayan tallafi na miliyoyin nairori ga al'ummar ƙaramar hukumar Bakori da yan bindiga suka raba da muhallansu suna gudun hijira a Bakori


Daga cikin abubuwan alkairin da matashin ya raba masu a yau akwai, katan din taliya guda 25, katan din makaroni guda 25, katan din omo guda 20


Sauran abubuwan da ya ba yan gudun hijirar tallafinsu sune, bubun shikafa yar gwamnati mai cin kilo 10 har buhu 50, masa buhu 100 ita ma mai cin kilo 10, buhun sukari manya guda 2 masu cin kilo 50kg kowannensu da kuma zunzurutun kudi har Naira N500,000 domin yin cefanen girki. 


Ba a nan ya tsaya ba, Ibrahim Dan Alkali ya kuma ba yan kwamiti na rabon kayan katan din taliya 5 na makaroni 5 da kuma Naira dubu hamsin kudin cefanensu.

Comments

Popular posts from this blog

Matashi Ya Kashe Maƙwabcinsa Saboda Rigimar Igiyar shanyar Katsina

ADC Coalition Stuns Kaduna: Secures 2 of 3 Constituencies in Landmark Victory

A Champion for Change: Commendation to Alhaji Hamisu Ado, Education Secretary, Nguru