Hukumar NEDC Ta Tallafa wa Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Yobe Da Kayayyakin Gini, Sauransu
Daga Sani Gazas Chinade Damaturu
Hukumar raya yankin arewa maso gabas ta NEDC tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Yobe, sun qaddamar da rabon kayayyakin gini ga al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa a qananan hukumomi 13 na jihar Yobe.
Shirin na da nufin tallafawa qoqarin farfaxo da tattalin arziki bayan da ambaliyar ruwa ta lalata gidaje da kuma kawo cikas ga rayuwar al'ummar wasu yankunan Jihar.
A yayin bikin qaddamar da tallafin da aka yi a Damaturu, Manajan Daraktan Hukumar NEDC, Mohammad Goni Alqali, wanda Kodinetan hukumar da ke Jihar Yobe, Farfesa Ibrahim Ali Abbas ya wakilta, ya jaddada illar da bala’in ya yi wa al’ummar wadannan yankuna da aka samarwa wannan tallafi.
“A Cewar sa hukumar NEDC ta samar da kayan rufi da sauran muhimman kayayyakin gini don taimakawa iyalai su sake gina gidajensu da wannan ambaliyar ruwa ta shafa.”
Baya ga kayayyakin gine-gine, hukumar ta kuma bayar da gudunmuwar kayan aikin ceto ga hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) domin inganta ayyukan tunkarar bala’in da ka iya faruwa a wannan damina da ake ciki ta bana ba fata ba.
Babban manajan na NEDC don haka ya bukaci masu ruwa da tsaki da su tabbatar da rarraba kayan agaji cikin gaskiya da adalci tare da yin kira da a yi amfani da kayan ta bin hanyoyin da suka dace kamar yadda aka tsara.
Da take kaddamar da rabon kayayyakin ginin ga al’ummomi 13 da ambaliyar ruwa ta shafa, kwamishiniyar ma'aikatar agajin da jinkai ta Jihar Yobe, Dokta Mairo Ahmed Amshi, ta yaba wa hukumar NEDC bisa qoqarin ta na bada waxannan kayan tallafi cikin lokaci, inda ta bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki na rage raxaxin waxanda ambaliyar ta shafa a wadannan yankuna a Qananan hukumomi 13.
Kwamishinan ta amince da ci gaba da qoqarin gwamnatin jihar wajen samar da agaji ga al’ummomin da abin ya shafa, da suka haxa da raba kayan abinci a baya, da magunguna, da matsugunan wucin gadi.
Dokta Mairi Amshi ta jaddada muhimmancin bin diddigi, inda ta yi qira ga shugabannin al’umma da hukumomin yankin da su sanya ido a kan yadda ake rarraba kayan da kuma amfani da su domin hana yin wata badaqala.
Ta buqaci wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da wannan tallafi ta hanyar amfani da kayan don manufarsu ta sake gina gidaje masu aminci da qwanciyar hankali a gare su.

Comments
Post a Comment