Gwamnatin tarayya tayi kunnen uwar shegu da bukatun talakkawa---Kwamared Abdulmajid Daudu
Daga Rabiu Sanusi
An bayyana Gwamnatin tarayya da cewa tayi biris da bukatun talakkawa na dawo da wasu tsaruka da suke saukakawa Al'ummar Najeriya ta fuska daban-daban.
Shugaban gamayyar kungiyoyin Yan kishin Kasa wadda akafi sani da(NIGERIA PATRIOTIC FRONT MOVEMENT) na Najeriya Kwamared Abdulmajid Yakubu Daudu ne ya bayyana haka a wani taron manema Labarai suka kira a ofishinsu.
Kwamared Daudu ya fara bayyana cewa na farko suna bukatar Gwamnatin tarayya data fara duba batun biyan diyyar wadanda suka rasa rayukan su a Zanga-zangar watan Ogusta daya gabata ga iyalan su.
Kwamared Daudu ya kuma bayyana cewa batun yadda gwamnati ta maida harkokin ciwo bashi yayi yawa da yazuwa yanzu Kasar na gab da durkushewa kamar yadda wasu kasashe suka samu kansu.
"Yanzu maganar da akeyi akwai Matsaloli Masu tarin yawa da suke barazana a wanna Kasar,kama daga hauhawar farashin kayan abinci,tsadar manfetu, da wannan gwamnati ta Kasa magance su."
"Idan kuka kalli maganar cin hanci da rashawa a wannan Kasa kullum Sabon salon yake dauka,maimakon a samu sauki kara gaba yake yi,babu wata hanya da zaka bayyana wannan gwamnati da zaka ce tana taimakon wannan Al'ummar ta.
Kwamared Abdulmajid Yakubu Daudu ya Kara bayyana cewa mafita a wannan Kasa yazuwa yanzu shine ta dawo da janye tallafin Manfetur da ta janye,sannan ta dawo da batun tsohon tsarin hanyar sadarwa ta NITEL dan saukakawa Al'ummar Najeriya.
Shugaban gamayyar kungiyoyin Yan kishin Kasar ya kuma bayyana bukatar dawoma da Manoma gonakin su da Makiyaya kuma a bar masu Dabbobin su su kiwata zai taimaka wajen Kara samun zaman Lafiya.
"Muna Kira da babbar murya ga Gwamnati tada mai da hankali wajen dawoma da Jama'a yaran su, da tun wancan lokacin Zanga-zangar sukayi batan dabo a fadin Kasar nan."
Kwamared Daudu yace har yanzu suna nan da Kudurin gudanar da wata Zanga-zangar Dan nusar da gwamnati na rashin cika wadannan alkawuran data daukar ma Talakawan ta, na rashin biyawa Yan Kasa bukatun da suka kamata.
Haka zalika Daudu ya Kara da cewa sukar Gwamnatin tarayya da hadiye Sauran Jam'iyyun adawa wanda hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin Siyasar Najeriya.
"Ya zaman wajibi a tsaida ciwoma Yan kasa bashi daga kasashen Duniya dan bashi da wani Amfani,kuma babu wata hanya da zamu bayyana shi da yake taimakon talakkawa.
Daudu ya kuma bukaci Gwamnati data maida mafi karancin Albashin karamin ma'aikaci zuwa naira dubu 250,000 ta yadda zai samu damar samun biyan wasu bukatun da yanzu suka gagare Shi musamman Abinci da Lafiya.
.jpg)
Comments
Post a Comment