Gwamnatin Jihar Yobe Ta Rufe kasuwannin 3 Dake Ci Mako-Mako
Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnatin jihar Yone ta bada sanarwar rufe wasu kasuwannin Jihar sakamakon wasu matakan tsaro zuwa wani lokaci da ba'a ayyana ba, kasuwannin sun hada da na garuruwan Katarko, Kukareta da kuma kasuwar Buni Yadi da ke ci mako-mako.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mai bada shawara kan harkokin tsaro ga gwamna Buni Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam RTD wadda ya bayyana hakan ga manema labarai a garin Damaturu, wadda ya ce an ayyana hakan ne da nufin ba da damar gudanar da wasu ayyuka kan harkokin tsaro a yankunan da nufin karfafa nasarorin da ake samu a yakin da ake yi da ta'addanci a jihar.
A cewarsa wannan matakin na wucin gadi ya zama dole domin cimma wasu tsare-tsare da aka sanya a gaba don inganta harkokin tsaro a yankunan da lamarin ya shafa da ma jihar baki daya.
"Ko da yake wannan shawarar na iya zuwa tare da sakamakonta, duk da haka ya zama dole daukar wannan mataki, don samun nasarar aikin."
A cewarsa, ana ci gaba da kokarin gaggauta aikin domin rage radadin rufe kasuwannin na wucin gadi ga rayuwar al'umma.
“Saboda haka muna rokon al'umma da su bada goyon baya, hadin kai da fahimtar juna domin samun nasarar aikin da ake yi domin samar da zaman lafiya da tsaro a jihar baki daya.
"Don haka muna tabbatar wa wadanda abin ya shafa cewa za a sake bude kasuwannin da aka rufe nan gaba, domin rufe kasuwannin na wucin gadi ne, nan da kwanaki masu zuwa da yardar Allah za'a sake bude su musamman da zarar lamurra sun Inganta.

Comments
Post a Comment