FUGA: Jami’ar Tarayya Gashuwa Ta Karrama Oluremi Tinubu, Buni, Wasu Manyan Mutane Da Digirin Girmamawa

 



Daga Sani Gazas  Chinade Damaturu 

Jami'ar Tarayya ta Gashuwa (FUGA) ta ba da digirin girmamawa na digirin digirgir a wani gagarumin ci gaba da aka samu tare da bikin hadaka na yaye daliban Jami'ar karo na farko na tarihin kafuwar jami'ar.


Bikin wanda aka gudanar da shi a ranar asabar ya kai ga yaye dalibai 3,449 da suka kammala karatun digiri na jami’ar, wadda ya samu karramawar gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, wanda ya kasance daya daga cikin fitattun mutane shida da aka baiwa lambar yabo ta digirin digirgir.


Haka kuma an baiwa uwargidan shugaban kasar Najeriya Sanata Oluremi Tinubu, Sanata Ibrahim Gaidam, Sanata Ahmad Ibrahim Lawal, Alhaji Bukar Goni Aji, da Justice C.G.  Wajid Muhammad, Sarkin Lafiya.


A nasa jawabin, gwamna Buni ya taya majalisar gudanarwar jami’ar, ma’aikata, da daliban jami’ar murna kan wannan taro mai dimbin tarihi da aka gudanar.


Gwamnan ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa kafa asusun ba da lamuni na ilimi na Najeriya (NELFUND), tare da karfafa gwiwar manyan makarantun jiha da su binciko ilimin sana’o’i domin samar da ayyukan yi ga matasa.


Ya kuma bayyana aniyar gwamnatin jihar na hada hannu da jami’ar domin tallafawa ci gaban dalibanta.


Tun da farko a nata jawabin, mataimakiyar shugabar jami’ar, Farfesa Maimuna Waziri, ta bayyana taron a matsayin bikin nuna nasarar ilimi, ci gaban cibiyoyin jami'ar ta FUGA.


“Wannan bikin ya nuna irin gagarumin ci gaba ga Jami’ar Tarayya ta Gashuwa, inda ya nuna muhimmancin hadin kai da goyon baya daga masu ruwa da tsaki wajen cimma burin jami’ar.


Ta kara da cewa, "Tare da bikin hadaka na farko, jami'ar na fatan samun makoma mai haske a gaba, sakamakon jajircewarta na inganta ilimi da ci gaban al'umma," in ji ta. 


Daga nan sai ta mika wasu bukatun jami'ar ga gwamnan  don neman daukin gwamnatin Jihar da suka hada da neman biyawa wasu masu gonakai da filayen da aka yi amfani da su wajen kafa jami'ar kudaden su da suka dade suna nema duk da cewar, gwamnatin Jihar na taimakawa jami'ar ta kowace fuska don ganin ta tsaya da kafafun ta wadda Kuma abin yabo ne.


Mataimakiyar shugabar jami'ar  ta yabawa gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu dangane da yadda ta ke taimakawa jami'ar matuka.

Comments

Popular posts from this blog

Matashi Ya Kashe Maƙwabcinsa Saboda Rigimar Igiyar shanyar Katsina

ADC Coalition Stuns Kaduna: Secures 2 of 3 Constituencies in Landmark Victory

A Champion for Change: Commendation to Alhaji Hamisu Ado, Education Secretary, Nguru