Murtala Sule Garo Ya Taya Al’ummar Musulmi Barka da Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447 AH


Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya taya daukacin al’ummar Musulmi barka da shigowar sabuwar shekarar Musulunci ta 1447 bayan Hijira.


A cikin sakon taya murna da ya fitar a ranar Litinin, Garo ya bayyana ranar 1 ga Muharram a matsayin lokaci mai matukar muhimmanci a duniyar Musulunci, wanda ke tunatar da darussan hijirar Manzon Allah (SAW) daga Makkah zuwa Madina da darussa na imani, jajircewa, da sadaukarwa.


Ya bukaci Musulmai da su yi amfani da wannan lokaci wajen karfafa kaunar juna, tausayi da jinkai a tsakanin al’umma, tare da jajircewa wajen gina zaman lafiya da hadin kai.


"Dukkan mu akwai rawar da za mu iya takawa don gina al'umma da tabbatar da zaman lafiya, kamar yadda addinin Musulunci ya koyar da mu,” in ji Garo.


Ya kuma yi addu’ar neman albarka da zaman lafiya a jihar Kano da Najeriya baki daya, tare da fatan Allah ya sanya sabuwar shekarar ta Musulunci ta kasance ta kawo wanzuwar zaman lafiya da arziki a jihar Kano da Kasa baki daya.


Barka da Sabuwar Shekarar Hijira!

Comments

Popular posts from this blog

Matashi Ya Kashe Maƙwabcinsa Saboda Rigimar Igiyar shanyar Katsina

ADC Coalition Stuns Kaduna: Secures 2 of 3 Constituencies in Landmark Victory

A Champion for Change: Commendation to Alhaji Hamisu Ado, Education Secretary, Nguru