GOBARAR YAN KASUWAR WAYA TA FIRM CENTER BABBAN IF'TILA'I NE - Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya aike da sakon jajantawa Yan kasuwar waya ta Firm Centre dake Kano.
Alhaji Aminu Ado Bayero cikin alhini ya bayyana damuwarsa bisa yadda aka samu asrar dukiyoyi a lokacin tashin gobarar.
Ya bayyana tashin gobarar da cewa wani if'tila'i ne daga ubangiji inda yayi addu'ar Allah ya mayar musu da mafificin abunda suka rasa.
Sarkin Kano Alhaji Aminu Bayero ya bukaci mahukunta dasu duba al'amarin tareda tallafawa Yan kasuwar da suka gamu da wannan if'tila'in.
Kazalika sarkin ya bukaci da aduba tare binciken abubuwan da suke haifar da irin wannan gobara lokaci zuwa lokaci domin maganin al'amurin.
Sa hannu.
Abubakar Balarabe Kofar Naisa Sakataren Yada labarai na Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP, CNOL

Comments
Post a Comment