Damunar Bana : Ministan Tsaro ya tabbatar da samar da Dakarun Tsaro ga Manoman Kasar nan

 




Daga Hussaini Yero 

Karamin Ministan Tsaro Bello Muhammed Matawalle ya tabbatar da samar da dakarun Tsaro da Jiragen sama ga Manoman Kasar a damunar Bana.

Ministan Matawalle ya bayyana haka ne a lakacin da yake amsasa tambayoyin manema labarai a gidansa da ke Maradun cikin Jihar Zamfara .


Matawalle ya bayyana cewa,Gwamnatin tarayya Karkashin Jagorancin Shugaban Kasa ta shiryar tsafa dan samar da Dakarun Tsaro, da jiragen sama da zasu shiga dazuzuka domin fatatakar "Yan ta'adda a fadin kasar nan .dan haka ina mai tabbatar wa Manoman Kasar nan, cewa  zasuyi noma cikin aminci da tsaro da da yardar Allah".


"Kuma ya tabbatar da cewa,hukumar tsaro na iyaka kokarinta wajan samar da tsaro a fadin Kasar nan.


Ministan Matawalle ya kuma yabawa wasu gwamnanin Kasar nan da suke taimakon Jami'an tsaron wajan yaki da "Yan ta'adda a jahohin su.ya kuma nuna takaicinsa ga wasu gwamnanin da suke ganin gazawar Jami'an tsaron a jahohin su, duk da basu basu gudunmuwar da ya kamata na magance matsalar tsaro.


Ministan ya kuma tabbatar da cewa, Shugaban Kasa Bula Ahmad Tunubu yayiwa 'yan Arewa adalci a bangaren mukamai da ya bada a Kasar nan.musamman a gefen Tsaro na mukamin Farar hula da masu kayan Sarki duk 'yan Arewa ne ke Jagorancin su.dan haka 'yan Arewa babu abunda ya kamata suyiwa gwamnati Ahmad Tunubu sai godiya da fatan alhairi.


Matawalle ya kuma yi kira ga al'ummar Kasar nan da su cigaba da yimata addu'a dan samun dawamamen zaman lafiya a kasa baki kiya .




Comments

Popular posts from this blog

Matashi Ya Kashe Maƙwabcinsa Saboda Rigimar Igiyar shanyar Katsina

ADC Coalition Stuns Kaduna: Secures 2 of 3 Constituencies in Landmark Victory

A Champion for Change: Commendation to Alhaji Hamisu Ado, Education Secretary, Nguru