Hukumar NEDC, Kungiyar MAKESAFE Sun Kaddamar Da Taron Bita Ga 'Yan Banga Kan Kasadar Abubuwa Masu Fashewa
Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Hukumar NEDC da hadin gwiwar kungiyar MAKESAFE mai kula da hakkokin bil-adama sun gudanar da taron bita na kwanaki biyu don horar da jami'an tsaron sa kai 158 na farar hula yadda ake iya gano abubuwa masu fashewa dangin bama-bamai don tsira da rayukan al'umma.
Wannan taro na bita dai an kaddamar da shi ne a babban dakin taro na CEDARS da ke garin Damaturu tare da halartar manyan jami'an gwamnatin Jihar Yobe.
Da ya ke bude wannan taro na bita dan majalisar dokokin Jihar mai wakiltar Gujba a zauren majalisar Honarabul Bulama Bukar wanda ya wakilci mataimakin kakakin majalisar dokokin Jihar Honarabul Ya'u Dachiya wadda shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin tsaro ya ce wannan taron bita kan wayar da kan jami'an tsaron sa kai (Vigilantees) kan harkokin abubuwa masu fashewa (Boms) abu ne da ya dace lura da yadda suka ba zu a cikin al'umma sakamakon tabarbarewar harkokin tsaro da Jihar ta yi fama da shi a baya na wajen shekaru 15.
Ya kara da cewar, lalle akwai bukatar da wadannan jami'ai da suka halarci wannan bita daga bangarori dabam-dabam na Jihar Yobe su mayar da hankali wajen samun ilimin wannan horo don su je su sanar da al'ummomin su a matsayin su na jekadu.
Ya kuma bada tabbacin goyon bayan majalisar dokokin Jihar Yobe ga bangarorin jami'an tsaro don ganin harkokin tsaro ya Inganta a jihar ta Yobe.
Dan majalisar ya ce shi harkokin tsaro ba wai ya tsaya ne kawai ga jami'an tsaro ko gwamnati kawai ba ya shafi kowa ta yadda dukkannin al'umma za su sa hannu wajen samun nasarar sa.
Shi ma da ya ke jawabi yayin bude wannan taro na bita, babban mai bada shawara kan harkokin tsaro ga gwamna Buni Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (RTD) ya ce makasudin wannan horo shi ne don a wayar da kan jama'a dangane da yadda kasadar da ake samu na abubuwa ma su fashewa wadda akwai bukatar da al'umma su sani don magance hadarin da ke tattare da shi.
Shi kuwa babban jami'in kungiyar MAKESAFE Guruf Kaftin Sadik Garba Shehu (RTD) ya ce a tarihin yake-yake dole na lokacin yaki da bayan sa akan samu an yi amfani da abubuwa masu fashewa wadanda ko da an kammala rakici ko yakin dole ne a samu wasu da yawan su an zubar da su ko kuma an jefa su amma ba su fashe ba amma kuma an yi watsi da su wadda a karshe sukan iya tashi su yi barna a cikin al'umma, domin ko da bayan yakin basasar Najeriya kusa shekaru hamsin da suka shude an samu ire-iren hakan wadda hakan ne ya sa mu ka yi yunkurin wayar da kan jama'a kan hakan lura da irin rikice-rikicen da aka sha fama da shi a wannan yanki na masu tada kayar baya.
A cewar sa hakan ne ya sa suka shirya wannan taron bita ga Jami'an tsaron sa kai da hadin gwiwar hukumar kula da sake gina yankin arewa maso gabas (NEDC) don ilimintar da su illar wannan abubuwa masu fashewa ga al'umma.
Ya bada misali da irin yadda matasan nan ma su sana'ar sayar da tsoffin karafu da akewa lakabi da masu ajakuta ke ta'ammali da tsoffin karafa yadda a wani lokacin akan tarar da yara sun dauko ire-iren wadannan abubuwa masu fashewa ba tare da sun sani ba da sunan karafunan ajakuta wadda a karshe in an yi rashin sa'a ya kan fashe ya illata lafiyar yaran kamar yadda ya faru a kwanakin baya a karamar hukumar Gujba yadda wani Yaro ya dauko ya fashe har ya cire masa yatsu .

Comments
Post a Comment