Ganduje Ya Bukaci Amfani Da Fasahar Zamani Don Yakar Ta'addanci,
Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da shawarar yin amfani da fasahar zamani wajen yaki da ta’addanci da ‘yan fashi a Najeriya.
Shugaban ya bayar da shawarar ne a ranar larabar da ta gabata a lokacin da ya jagoranci mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa a ziyarar jaje ga gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni a kan harin da aka kai wa rundunar sojijin barikin soja da ke Buni Gari.
Ganduje ya ce dole ne yaki da ‘yan tada kayar baya da ‘yan fashi da makami su tafi tare da hakikanin lokaci domin samun nasara.
Ya bayyana cewa abin takaici ne irin yadda ‘yan tada kayar baya da ‘yan fashi suke aikata munanan ayyuka a fadin kasar nan.
“A yanzu za a yi amfani da albarkatun da ake da su don maye gurbin irin kayan aikin da aka lalata."
Da ya ke mayar da jawabi, gwamna Buni ya ce gwamnati a matakai daban-daban na duba yadda ake amfani da fasahar zamani wajen yaki da 'yan ta'adda.
"Mu, a matakin kasa da gwamnonin yankin Tafkin Chadi, muna yin nazari sosai kan yadda makiya ke amfani da jirage marasa matuka aikata ta'assar wadda dole mu hada kai jami'an tsaro don duba matsalar," in ji Buni.
Ya ba da tabbacin cewa za a tattauna hakan a mataki mafi girma musamman da shugaban kasa domin dakile ayyukan tada kayar baya da ‘yan bindiga.
"Wannan matsala ce ta kasa domin a lokacin da suka kai hari a sansanin soji da kuma kwace makamai, ba za a iya sanin inda za a yi amfani da su ba, don haka ya kamata a dauki wadannan hare-hare a matsayin hare-hare ga al'ummar kasa baki daya ba wai Jihar Yobe kadai ba."

Comments
Post a Comment