Cikar Shekaru 6: Mukan Taimakawa Harkokin Ilimi, Noma, Don Matasan Mu Su Amfana-Buni
Daga Sani Gazas Chinade Damaturu
A bikin cikar sa shekaru 6 cur akan mulkin Jihar Yobe gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe da aka gudanar a ranar Alhamis din da ta gabata ya bayyana irin gagarumin ci gaban da aka samu akan harkokin ilimi da noma, inda ya ce akasarin wadansa suka amfana a wadannan fannoni guda biyu matasa ne.
Da ya ke jawabi a yayin wannan taro na bikin cikar sa shekaru 6 akan mulki da aka gudanar a babban dakin taro na Banquet da ke gidan gwamnatin Jihar a garin Damaturu tare da ma su ruwa da tsaki na Jihar, gwamnan ya bayyana kudirin sa na cigaba da Inganta harkokin da suka shafi matasa da kuma sauran fannonin da tunin gwamnatin sa ta yi nisa cikin su kamar fannin noma, kiwon lafiya, kasuwanci, tsaro da makamantan su.
Taron wanda ofishin mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin talabijin, Rediyo, da kafafen yada labarai na zamani, Dr. Ibrahim Yabani, ya shirya yadda gwamnan ya amsa tambayoyin da wasu al'ummominn Jihar hade da 'yan jaridu da kungiyoyin farar huka daga kananan hukumomin Jihar 17 suka yi wadda nan ta ke gwamnan ke amsa musu tambayoyin da suka masa ido da ido.
A nasa jawabin, Gwamna Buni ya jaddada cewa taimakawa matasa na da matukar muhimmanci wadda kamar yadda ya ambata hakan ne ya ba shi karfin gwiwar kara Inganta harkokin ilimi wadda matukar matasa sun samu Ilimi to kuwa batun zaman banza zai kau kasancewar da sun samu Ilimi mai amfani gwamnatin na da karfin gwiwar samar musu da aikin yi ta kowace irin fuska.
Gwamnan ya ce, akalla gwamnatin Jihar a duk wata takan kashe zunzurutun kudi sama da naira miliyan 600 wajen ciyar da daliban makarantun kwana wadanda dukkan su matasa ne kana gwamnatin sa ta tura matasa sama da 100 zuwa kasar Indiya don samun horo akan karantun likita wadda a yanzu haka matasan sun kammala sun dawo Jihar har an samar musu aikin yi a asibitocin Jihar.
Kan bangaren noma ma haka lamarin ya ke domin gwamnatin sa ta samar wa matasan kayayyakin gudanar da noman zamani, wadda kuma kwalliya tunin ta biya kudin sabulu.
Haka nan ta bangare tsaro nan ma haka lamarin ya ke domin gwamnatin ta akullum ta kan yi abin da ya dace dangane da harkokin na tsaro musamman ta wajen samarwa jami'an tsaron Jihar hade da na Sibilyan JTF kayan aikin da suka hada da motocin sintiri da sauran su don ganin an dakile barazanar da masu tada kayar baya ke yi ga al'ummar Jihar.
Ta fuskar gina titunan karkara ma gwamnatin sa ba ta yi kasa a gwiwa ba kasancewar yana da matukar muhimmanci wajen harkokin Inganta kasuwanci, aikin noma hada kan al’umma musamman a kananan hukumomin Potiskum, Damaturu, Nguru, Gashua, da Geidam da aka gina musu hanyoyin mota don kara alatu a garuruwan da kuma gina hanyoyin karkara a kananan hukumomin Jihar.
Da yake amsa tambayoyi daga mahalarta taron, Buni ya bayyana cewa, yawan gina hanyoyin mota ba wai rage tsadar sufuri ba ne, har ma yana kara habaka tattalin arzikin yankunan gaba daya ta hanyar saukakawa manoman kawo amfanin gonakinsu zuwa kasuwannin Jihar.
Ya kara da cewa, "Hanyoyin da muka gina ba hanyoyi ba ne kawai; suna da matukar muhimmanci ga bangaren noman mu, don tabbatar da cewa amfanin gonakinmu ya isa ga masu amfani da shi yadda ya kamata."
Gwamnan ya amince da sauran kalubalen amma ya nuna kwarin guiwa game da ayyukan ci gaba da ake yi a jihar.
Ya nanata kudurin gwamnatinsa na samar da yanayi mai kyau ga ci gaba, kirkire-kirkire, da ci gaba mai dorewa.
.jpg)
Comments
Post a Comment