Gwamna Buni Ba Shi Da Wani Shiri Na Shiga Hadakar Atiku, in ji Kakakin Gwamna


Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu 

An bayyana cewar, gwamna Mai Mala Buni na Yobe ba shi da wani shiri ko cikin kawancen shugabannin adawa da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ke jagoranta.


Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Yada Labaran gwamnan Alhaji Mamman Mohammed ya fitar a Damaturu ranar Asabar.


Aminiya  ta ruwaito rahoton cewa wani sako da ya bayyana a kafofin yada labaran zamani na yanar gizo wadda wadda wani wai shi George Udom ke ikirarin cewa Buni da wasu gwamnonin APC hudu sun kammala shirye-shiryen sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP da kuma shiga kawancen jam’iyyar kafin zaben 2027.


Kakakin na gwamna ya siffanta saƙon a matsayin ƙirƙira marar tushe, hasashe marar tushe da mummunan zaton da ya saba ka'Ida abin Allah wadarai.


Ya ce babu wani lokaci da marubucin wannan labari ya taba kusantar gwamnan don tunanin zai iya yin hasashen yunkurin siyasar gwamnan ballantana ya hararo makomar sa a siyasance.


“Buni dan jam’iyyar APC ne, ba wai talakan APC ko  gwamnan APC bane kawai, ta kowane fanni Jam'iyyar APC na nan tamfar jini da tsoka a gare shi, in ji Mamman Mohammed.


“Gudunmawar da ya bayar wajen gina jam’iyyar APC a matsayin sakataren kasa na wa’adi biyu kuma shugaban rikon jam’iyyar na kasa wanda ya jagoranci kwamitin taron jam’iyyar ya sa ya zama na musamman, kuma ba za a iya hasashen tunaninsa na ficewa daga jam’iyyar ba,” inji shi.


Mohammed ya ce marubucin wannan labarin cin kanzon kurege ya tafka babbar karya kan makomar gwamna Buni a siyasance.

Comments

Popular posts from this blog

Matashi Ya Kashe Maƙwabcinsa Saboda Rigimar Igiyar shanyar Katsina

ADC Coalition Stuns Kaduna: Secures 2 of 3 Constituencies in Landmark Victory

A Champion for Change: Commendation to Alhaji Hamisu Ado, Education Secretary, Nguru