Gwamnatin Jihar Katsina Ta Amince Da Kafa Sabuwar Tashar Zangon FM A Jihar
Daga Fatima Mukhtar Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Katsina, Dakta Salisu Bala Zango, ya bayyana cewa gwamnati ta amince da kafa sabuwar tashar rediyo mai gajeren zangon FM a wannan shekarar. Dakta Salisu Ya bayyana hakan ne yayin kare kasafin kuɗin ma’aikatarsa a matakin Maaikatar kula da kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki dake gudana a tsohuwar Fadar Gwamnati. A cewar sa, aikin kafa tashar FM ɗin zai ci wa gwamnati kimanin naira miliyan 366, kuma ana sa ran hakan zai ƙara haɓaka inganci, yawan masu sauraro, da faɗaɗa isar da shirye-shirye da manufofin gwamnati. “Mun samu amincewar kafa sabuwar tashar FM jiya, kuma muna cikin shirye-shiryen tabbatar da cewa ta fara aiki cikin wannan shekara,” in ji shi. Kwamishinan ya bayyana cewa, da zarar an kaddamar da tashar FM ɗin, za a samu damar cika burin samun kudin shiga har naira miliyan 300 daga tashar AM mallakar jihar. Haka kuma, kwamishinan ya bayyana shirin gwamnati na sanya samarwa gidan Radion jihar makamashi ...